1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin bunksa da tattalin arzikin yankin Asiya

Ramatu Garba Baba AMA
November 16, 2020

Kungiyar kasashen yankin Asiya da Pacific sun kulla yarjejeniyar kasuwancin bai daya mafi girma a duniya don kara bunkasa tattalin arzikisu biyo bayan shafe tsawon shekaru suna tattaunawa.

https://p.dw.com/p/3lMuh
Indonesien Bogor | Joko Widodo unterschreibt Handelsabkommen
Hoto: Muchlis Jr/ Biro Pers Sekretariat Presiden

Yarjejeniyar ta hada kan kasashe goma sha biyar mambobin kasashen yankin Asiya da Pacific da ke da al'umma fiye da mutum biliyan biyu, masu kaso talatin cikin dari na tattalin arzikin duniya, an kwashe kusan shekaru goma kafin a kai ga cimma matsayar, kana kasashen da ke karkashinta sun hada da Chaina kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, mambobinta suna cike da fatan ganin kwalliya za ta biya kudin sabulu a sakamakon sabbin matakai na sassauta dokokin kasuwanci da zai kai ga bunkasar tattalin arzikin yankin.

Yunkurin bunkasa tattalin arziki

Indonesien Bogor | Joko Widodo unterschreibt Handelsabkommen
Hoto: Muchlis Jr/ Biro Pers Sekretariat Presiden

Abubuwan da ake son mayar da hankali akai sun hada kokarin habakka tattalin arziki da kawar da shingen kasuwanci tsakanin kasashen yankin Asiya musanman inda aka sami sabani kan rikicin kan iyaka. Firaiministan Viatnem Nguyen Xuan Phuc mai masaukin baki a yayin jawabinsa ya jaddada mahinmancin yarjejeniyar da ya ce bama ga kungiyar kadai ba, tana da kwakwarar rawar da za ta taka a bunkasar sauran kasuwannin duniya. 

Karin Bayani: Rikicin Kasuwanci tsakanin Amirka da China

Yarjejeniyar ta shirya matakai da dama ciki har da kokarin rage farashi da daidaita dokokkin cinikayya a tsakanin juna, masu sharhi na ganin mataki ne da zai kara sanaya kasar Chaina a sahun gaba, da karfin ikon shata dokokin cinikayya ga kasashe kamarsu Japan da New Zealand

Yarjejeniya mai dimbin tarihi  Kasashen da suka rattaba hannu a yarjejeniyar sun hadar da Chaina, da Japan da Koriya ta Kudu  da Australiya da New Zealand da kuma sauran kasashen yankin Asiya da suka hada da Burunai da Vietnam da Laos da Kambodiya da Thailand da Myanmar da Malaysiya da Singapore da Indonesiya da Philippines. Kasar Indiya na ciki kafin ta fice bayan korafin da ta yi a game da rashin ingancin kayayyakin da ta ke siya daga Chaina amma mambobin sun ce da sauran dama in har tana da sha’awra sake shiga.

Indonesien Bogor | Joko Widodo unterschreibt Handelsabkommen
Hoto: Muchlis Jr/ Biro Pers Sekretariat Presiden

Ana kuma ganin Chaina za ta yi nasarar tsaya wa da kafafunta ba tare da dogaro da sauran hajjioji na sauran kasuwannin duniya ba kamar Amirka da suka dadde suna takunsaka ba.