Rikicin Kasuwanci tsakanin Amirka da China bai shafi Afirka ba | Siyasa | DW | 28.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin Kasuwanci tsakanin Amirka da China bai shafi Afirka ba

Abu ne mai wahala takaddamar kasuwanci tsakanin China da Amirka ta shafi kasashen nahiyar Afirka kai tsaye sosai ba, za ma a iya cewa gaba ta kai su.

 Musamman ma yanzu da suke shirin kaddamar da batun kasauwanci mara shinge a tsakanin kasashen nahiyar, abin da ake kira da tuwona maina ke nan. Shugabannin kasashen na China da Amika dai, na shirin ganawa a gefen taron kasashe 20 masu karfin tattalin arziki na duniya wato G20, da ke gudana a birnin Osaka na Kasar Japan.Gabanin ganawarsu a taron kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya, shugaban Amirka Donald Trump da takwaransa na China Xi Jinping sun bayyana cewar za su tattauna da nufin shawo kan matsalar takaddamar kasuwancin da ke tsakaninsu. A yayin da Shugaba Trump na Amirka ya bayyana cewa yana ganin ganawar za ta haifar da makoma mai kyau, a nasa bangaren Shugaba na China ya ce akwai bukatar su samar da yanayin kasuwanci na daidaito  da kuma bunkasa harkokin fasaha da sadarwa kana su tabbatar da cewar sun kare martabar yanayin masana‘antu a duniya baki daya. 

 

Sauti da bidiyo akan labarin