1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yara na nuna fushi kan sauyin yanayi

March 15, 2019

Matsalar sauyin yanayi da duniya ke fama da ita, ta sanya yara fitowa daga wasu don jan hankalin manyan saboda sama wa matsalar magani saboda rayuwarsu ta nan gaba.

https://p.dw.com/p/3F6K6
Hamburg Greta Thunberg bei Klimastreik
Hoto: Getty Images/A. Berry

Dubban yara 'yan makaranta ne suka fara wata zanga-zangar neman shugabannin kasashe da su gaggauta daukar matakai kan matsalar nan ta sauyin yanayi da duniya ke fama da ita.

Yaran daga kasashen Ostireliya da kuma New Zealand, na fatan zanga-zangar ta su za ta mamaye birane dubu da 500 cikin kasashen duniya sama da 100.

Manyan na gobe sun ce za su kaurace karatu don janyo hankalin duniya kan matsalar ta yanayi da suka ce su ne abin zai fi taba wa rayuwa nan gaba.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta goyi bayan zanga-zangar tana mai bayyana aniyar yaran 'yan makaranta da cewar kyakkyawa ce. Ita ma Firaministar kasar New Zealand Jacinda Ardern, ta yaba da yunkurin.