1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman dauki ga yaran Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Yusuf Bala Nayaya MNA
November 30, 2018

A shekaru biyar na rikici a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya kimanin kashi biyu daga cikin uku na yara na cikin matsananciyar bukatar a kai masu agaji a cewar Asusun UNICEF a wannan rana ta Juma'a.

https://p.dw.com/p/39B62
Zentralafrikanische Republik Unterernährte Kinder
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Delay

Tun da yaki ya barke a 2013 fiye da mutane miliyan daya ne suka guje wa muhallansu yayin da kusan miliyan uku daga kusan miliyan biyar ke cikin tsanani na bukata. A cewar Asusun UNICEF muddin al'umma ba su koma gonakinsu ba, babu makawa a shekaru masu zuwa za a fuskanci babbar matsala ta yunwa a wannan kasa.

A cewar rahoton fadakarwar na Majalisar Dinkin Duniya kan halin da yara kananan ke ciki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wacce yakin da take ciki bai samun kulawar da ta dace, kimanin yara dubu 43 da ke kasa da shekaru biyar za su samu kai a yanayi na fuskantar barazanar mutuwa saboda rashin abinci mai gina jiki a shekarar 2019. Rashin abincin dai na zame masu sila ta saurin samun cututtuka kamar maleriya da kyanda ko ma amai da gudawa.