'Yankin Scotland na neman ballewa daga Birtaniya
March 28, 2017A ranar Laraba ce dai (29.03.2017) Firaministar Birtaniya Theresa May za ta mika takardar fara aiwatar da shirin ficewar kasar daga kungiyar Tarayyar Turai a hukumance. Tun dai a ranar Laraba da ta gabata ce ya kamata majalisar ta Scotland wadda masu rajin samun mulkin kai suka fi yawa a cikinta ta yi wannan zama, amma kuma harin da aka kai a majalisar dokokin kasar ta Birtaniya a Westminster da ke birnin London ya sa aka dage batun kada kuri'ar.
Yankin na Scotland dai na adawa da ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai, wanda a lokacin kada kuri'ar neman ficewa daga Tarayyar ta Turai, yankin ya nuna adawarsa da kashi 62 cikin 100, inda ake ganin idan har suka yi nasarar ballewa, to za su shiga cikin kungiyar ta Tarayyar Turai matakin da ake gani tamkar wani sare kafafu ga Birtaniya.