Yanayin kallon kwallon duniya a Najeriya | Zamantakewa | DW | 11.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Yanayin kallon kwallon duniya a Najeriya

Jami'an tsaron jihar Plateau sun bayyana cewar za su karfafa tsaro a cibiyoyin kallon kwallo, don tabbatar da cewar ba a fuskanci hare-hare lokacin kofin duniya na Brazil ba.

Hukumomin sun dauki matakan na tsaro ne sakamakon hare haren da aka kai cibiyoyin kallon kwallon kafa a Jos, lamarin dake neman janyo tsoro a zukatan masu sha'awar wannan wasa. To sai dai kakakin rundunar 'yan sanda ta jihar Plateau Felicia Aslem, ta ce za su " samar da cikkaken tsaro a dukkanin cibiyoyin kallon kwallon kafa dake cikin jihar a lokacin gasar ta kofin duniya. Hakan ya zama wajibi don tabbatar da ganin mun kare daukaccin masu kallon kallon:"

Shugaban kungiyar masu gidajen kallon kwallon kafa a jihar Plateau Zakari Mohammed, ya shaida wa DW Hausa cewar sun yi zama a lokuta daban daban da jami'an tsaro gabanin gasar ta kofin duniya, don daukan matakan da sua wajaba.

A kwanakin baya ne dai wasu mahara suka nufin wani gidan kallon kwallon kafa a nan Jos, sa'ilin da ake gassar karshe ta kofin zakarun Turai. Ko da shike basu cimma gidan kallon ba, amma kuma bam din ya tashi.

To amma kuma ra'ayoyi sun banbanta tsakanin masu sha'awar zuwa kallon a gidajen da ake nuna wassannin. Ranar Alhamis ta wannan makon ne dai ake soma gasar ta kofin duniya a kasar Brazil.

Mawallafi: Abdullahi Maidawa daga Jos
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe