′Yan wasan Kenya da shan kwayoyi a gasar Olympic | Labarai | DW | 26.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan wasan Kenya da shan kwayoyi a gasar Olympic

Koki Manunga da Joyce Zakary a ranar Laraban nan kungiyar kasa da kasa da ke shirya wasannin na motsa jiki IAAF ta gano cewa suna ta'ammali da kwayoyi masu kara kuzari.

Maasai Olympics in Kenia

'yan wasan tsere daga Kenya

Wasu 'yan kasar Kenya da suka shiga gasar guje-guje da ake yi cikin wasannin Olympic a kasar China sun karbi takardar da ke haramta musu shiga irin wannan wasani a nan gaba.

Koki Manunga da Joyce Zakary sun karbi wannan takarda a ranar Laraban nan bayan da kungiyar kasa da kasa da ke shirya wasannin na motsa jiki IAAF ta gano cewa suna ta'ammali da kwayoyi masu kara kuzari.

A cewar jawabin da hukumar ta IAAF ta fitar 'yan wasan na Kenya masu shiga gasar guje-guje an gano mu'ammalarsu da magunguna masu kara kuzari bayan gwajin da aka yi musu a otel din birnin Beijing a ranakun 20 ga watan Agusta da ranar 21 ga watan na Agusta.