'Yan wasan Bundesliga 10 mafi karancin shekaru
Kwana guda bayan ya cika shekaru 16, an saka Youssoufa Moukouko a karawa tsakanin Dortmund da Hertha Berlin. Yanzu shi ne lamba daya a jerin 'yan wasan kwallon kafa mafi karancin shekaru a gasar Bundesliga ta Jamus.
1. Youssoufa Moukoko - Shekaru 16 da kwana 1
Tun wasu shekaru Youssoufa Moukoko ke buga kwallo da 'yan wasa da suka girme shi: Yana da shekaru 13 yake cikin rukunin 'yan kasa da shekaru 17 na Dortmun, da shekaru 15 ya shiga rukunin 'yan kasa da shekaru 21 na BVB. Godiya ga sauyin dokoki, dodon ragar dan shekaru 16, yana iya wasa a Bundesliga. Kwana guda bayan ya cika shekaru 16, Lucien Favre ya saka shi a karawa da Hertha Berlin.
2. Nuri Sahin - shekaru 16 da kwana 335
A kakar 2005/06 Borussia Dortmund ta kara yawan matasa da ke mata wasa saboda matsaloli na kudi. Maihoras da 'yan wasan kungiyar Bert van Maarwijk ya dauko Sahin daga rukunin B na matasa zuwa na manya, inda a mako na daya ya saka shi a karawa da Wolfsburg (hoto). Sahin ya yi wasa tsawon shekaru 10 a rukunin manya na BVB (2005-2007, 2008-2011, 2013-2018). Yanzu yana wasa a Antalyaspor.
3. Yann Aurel Bisseck - shekaru 16 da kwana 362
A ranar 26 ga watan Nuwamban 2017 dan wasan bayan, ya yi wasansa na farko karkashin koci Peter Stöger a karawa da Hertha BSC (0:2). A jimilce Bisseck ya yi wasa sau uku a kakar wasansa na farko a Bundesliga. Bayan da FC Kolon ta yi kasa, ba a ba shi wata kulawa ba. Ya yi sauyin sheka zuwa Holstein Kiel, a can ma bai yi wani abin kirki ba. Yanzu yana taka leda a Victoria Guimaraes a Portugal.
4. Florian Wirtz - shekaru 17 da kwana 15
Tun gabanin ya fara wasa a Bundesliga sunansa ya yi tashe a kafafan yada labarai. Dalili: Canji daga FC Collogne zuwa Bayer 04 Leverkusen da aka yi cece-kuce a kai. 'Yan Collogne sun yi fushi yadda Leverkusen ta dauke musu mai baiwar wasan kwallo. A Leverkusen Wirtz ya gamsar da koci Peter Bosz saboda sauri da iya murza leda. A ranar 18 ga Mayun 2020, a karon farko ya yi wasa a karawa da Bremen.
5. Jürgen Friedl - shekaru 17 da kwana 26
A lokacin da mai tsaron ragar Frankfurt ya yi rauni, a karawa a gida da Hannover (5:1) a ranar 20 ga Maris 1976, an saka Friedl yana tsaro na hudu a Eintracht. Tsawon shekaru 30 shi ne dan wasa mafi karancin shekaru a Bundesliga, kafin Sahin ya canje shi. Wasanni uku kadai Friedl ya yi a Bundesliga, ya kuma ci duka. Tsayinsa na mita 1,75 ya yi wa Eintracht gajarta, ba a sabunta kwantaraginsa ba.
6. Ibrahim Tanko - shekaru 17 Jahre da kwana 62
Dan kasar Ghana a shekarun 1990 da shi da Lars Ricken (shekara 18) sun zama masu kai hari a kungiyar Borussia Dortmund. A ranar 24 ga Satumban 1994, Tanko ya yi wasan farko a karawa tsakanin BVB da Stuttgart 5:0 (hoto). Sai dai bai kai matsayin da ake bukata ba a tsukin shekaru bakwai da ya yi a Dortmund. An soke kwantiraginsa bayan an same shi da laifin shan tabar wiwi. Ya koma Freiburg.
7. Giovanni Reyna - shekaru 17 da kwana 66
Da kwana hudu ya dara Tanko lokacin da Giovanni Reyna ya yi wasan farko da Dortmund. A ranar 18 ga Janairun 2020. An saka shi a karawa da FC Augsburg. Reyna, wanda mahaifinsa Claudio ya taba yi wa Leverkusen da Wolfsburg wasa a Bundesliga, tun a 2019 yake Dortmund. Dan asalin kasar Amirka ya samu horonsa a matsayin matashi dan kwallon kafa a New York City FC, inda mahaifinsa ya taba zama darakta.
8. Jude Bellingham - shekaru 17 da kwana 82
Matashin dan Ingila, tun yana kungiyar kwallon kafa ta Birmingham City ya nuna kwarewa. Bayan da Bellingham ya bar Birmingham, kulob din ya sanar cewa ba zai ba wa kowane dan wasa lambar jersey dinsa ba. A Dortmund matashin ya shiga jerin rukunin matasa masu baiwar iya kwallo. A karawa da Borussia Mönchengladbach a Satumbar 2020, ya samu damar yin wasansa na farko.
9. Josha Vagnoman - shekaru 17 da kwana 89
Babansa dan Cote d'Ivoire babarsa Bajamushiya, ya girma a Hamburg. A 2010 yana da shekaru tara ya shiga sashen matasa na Hamburger SV. A watan Maris na 2018, ya yi wasan farko da uwar kungiyar ta HSV a karawa da FC Bayern, sai dai HSV ta sha kashi da ci 6-0. A kakar wasa, dan wasan bayan da kungiyarsa ta HSV sun yi kasa zuwa Bundesliga ta biyu. Har yanzu yana wasa a Hamburg.
10. Simon Asta - shekaru 17 da kwana 107
A ranar 12 ga Mayun 2018, Freiburg na da ci 2:0, mai horas da 'yan wasan Augsburg na lokacin Manuel Baum ya cire dan wasan tsakiya Jan Moravek ya saka Simon Asta dan wasan baya, ana sauran mintuna 10 da kammala wasa. Lokacin mai tsawo, ya kasance wasan Asta daya tilo a Bundesliga. Shekara guda bayan nan ya bugawa FCA a makon karshe na kakar Bundesliga. Yana yi wa 'yan kasa da shekara 19 wasa.