1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawayen Yemen sun kwace kwalejin sojoji

December 5, 2014

Babu dai wasu bayanai kawowa yanzu da suka fita daga bangaren yan tawayen kungiyar Hausiyin da bangaren gwamnatin kasar ta Yemen a daidai lokacin kan sabon lamarin

https://p.dw.com/p/1E002
Bildergalerie Jemen Eroberung der jemenitischen Hauptstadt Sanaa
Hoto: DW/S. Alssofi

'Yan tawayen kungiyar Hausiyin mabiya darikar Shi'a a kasar Yemen, sune suka aka bada labarin cewa, sun kwace wata makarantar horar da aikin soji a birnin Sana'a fadar gwamnatin kasar ta Yemen, kamar yadda wani da ya shaida yadda lamarin ya auku ya bayyana.

"Masu dauke da bindigar sun sami damar shiga kwaleji ba tare da fiskantar wata tirjiya ba daga jami'an tsaro masu gadin makarantar kamar yadda wani dalibai da ke samun horo da baya so a bayyana sunansa ya shedar"

Ya kara da cewa ya zuwa yanzu mayakan na Hausiyin suke iko da babbar kofar shiga kwalejin. Wannan yunkuri dai ana kallon wani kara samun karfi ne ga 'yan tawayen a babban birnin kasar.

Babu dai wasu bayanai kawowa yanzu da suka fita daga bangaren na Hausiyin da bangaren gwamnatin kasar ta Yemen a daidai lokacin da Hausiyin ke ci gaba da mamayar gine-ginen gwamnati a birnin na Sana'a.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Usman Shehu Usman