Yan tawayen Ogaden a Ethiopia sun tsagaita wuta | Labarai | DW | 02.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan tawayen Ogaden a Ethiopia sun tsagaita wuta

Yan tawayen yankin Ogaden na ƙasar Ethiopia, sun ƙaddamar da wani mataki na tsagaita wuta, domin baiwa komitin Majalisar Ɗinkin Dunia damar gudanar da bincike a game da zargin da su ke yi wa gwamnatin ƙasar da cin zarafin jama´a a yankin na Ogaden.

A cikin sanarwar da su ka fido yan tawayen sun yi kira ga komitin na ƙasa da ƙasa, ya ziyarci dukkan lugunan da ya ke buƙata na yankin Ogaden, domin tattara shaidu.

A cewar ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin bani adama, a tsukin wattani 2 da su ka gabata, gwamnati ta maitsa ƙaimi wajen gana azaba ga jama´ar yankin Ogaden, a yunƙurin ta na murƙushe yan aware.

Ya zuwa yanzu, a ƙalla mutane 74 su ka rasa rayuka a sakamakon harin na dakarun gwamnati.

Tawagar ta Majalisar Ɗinkin Dunia da ta ƙunshi jami´ai 14, ta fara rangadi tun ranar alhamis da ta wuce, domin tantance gaskiyar wannan al´amari.