'Yan tawayen Chadi za su zauna da sojoji | Labarai | DW | 23.07.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan tawayen Chadi za su zauna da sojoji

'Yan tawayen Chadin sun ce a yanzu za su koma tattaunawar da ake yi da su ba tare da wani karin bayani ba. Tun da farko sun zargi gwamnatin wucin gadi ta kasar da kawo musu cikas a tattaunawar da ake da su a Katar.

'Yan tawayen Chadi sun ce za su sake shiga tattaunawar sulhu da gwamnatin rikon kwaryar kasar bayan ficewar da suka yi daga tattaunawar a makon da ya gabata. 

Matakin da suka sanar a ranar Jumma'a ya kara kyautata fatan shigarsu cikin tattaunawar kasa da aka shirya gudanarwa a watan gobe na Agusta a kasar ta Chadi. Tattaunawar ce ake sa ran za ta share fagen wareware rigingimun kasar kafin gudanar da zabe  bayan da shugaban rikon kasar Mahamat Idriss Deby ya kwace iko da kasar jim kadan bayan mutuwar mahaifinsa a shekarar da ta gabata.