1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ji duriyar 'yan tawayen Chadi da ke tsare

Gazali Abdou Tasawa
January 23, 2019

A kasar Chadi wasu shugabannin 'yan tawayen kasar guda biyu sun bayyana a karon farko tun bayan da gwamnatin Nijar ta mika su ga hannun mahukuntan kasar ta Chadi bayan kama su a garin Agadez.

https://p.dw.com/p/3C41g
Tschad Präsident Idriss Deby
Hoto: Getty Images/AFP/L. Marin

A karshen shekara ta 2017 ne kasar ta Nijar ta kama 'yan tawayen na kungiyar CCMSR mai da'awar ceto kasar Chadi daga mulkin kama karya su uku tare da mika su a hannun mahukuntan kasar ta Chadi. 

Sai dai tun daga wancan lokaci gwamnatin kasar ta Chadi ta musanta karbar wadannan 'yan tawaye daga hannun kasar ta Nijar. Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP ya ruwaito a wannan Laraba wata majiyar tsaron kasar ta Chadi na cewa an tsinkayi biyu daga cikin wadannan 'yan tawaye wato Hassan Boulmaye tsohon shugaban kungiyar tawayen ta CCMSR da kuma Ahmat Yacoub Adam tsohon kakakin kungiyar a gidan kurkuku na tsakiyar birnin Ndjamena, a yayin da na uku mai suna Abdraman Issa wanda da ma ke fama da cutar siga ya rigaye mu gidan gaskiya a cewar majiyar tsaron kasar ta Chadi.