′Yan tawaye sun yi garkuwa da matukin jirgin sama | Labarai | DW | 15.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan tawaye sun yi garkuwa da matukin jirgin sama

'Yan tawaye a Siriya sun sanar da kakkabo jirgin yakin gwamnati tare da yin garkuwa da matukin jirgin da suka nuna a hoton bidiyo cikin tsanani na rashin lafiya.

Kungiyar 'yan tawaye mai suna Osoud al Sharqiya ta ce ita ta harbo jirgin yakin gwamnati tare da yin garkuwa da matukin jirgin, a sanarwar da kakakin kungiyar Saad al Haj ya fitar ya ce matukin jirgin na hannunsu duk da cewa ya ji rauni kakakin ya ce suna ba shi magani, ya kuma kara da cewa za su ci gaba da ba shi kulawa kamar yadda dokokin duniya suka amince a yi a yanayi irin wannan, sai dai babu karin bayani na yadda za su yi da matukin jirgin in har ya sami sauki. A wani hoton bidiyon da kungiyar ta fitar ta nuna matukin jirgin mai suna manjo Ali al Hilwa cikin tsanani na rashin koshin lafiya.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Syrian Observatory for Human Rights ta tabbatar da labarin kakkabo jirgin da kuma garkuwa da aka yi da matukin jirgin a wani yankin da ta ce an cimma yarjejeniya na tsagaita wuta. Mutane fiye da dubu dari uku ne suka mutu tun bayan barkewar yakin basasa shekaru fiye da biyar a kasar ta Siriya.