′Yan tawaye na gwabza fada a Siriya | Labarai | DW | 19.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan tawaye na gwabza fada a Siriya

Bangarorin 'yan tawayen na gwabza kazamin fada a tsakanin junan su, kungiyoyin sa'aido a kasar sun ce gumurzun wutan ya yi sanadiyar mutuwar mutane 11 daga dukkanin banagarorin biyu da wasu fararen hula uku.

Barkewar rikici tsakanin kungiyoyin biyu na zuwane kwanaki kalilan bayan da wata kungiyar 'yan tawaye ta kaddamar da kafa tuta a yankin Idlib, an dai kwashe tsawon sa'anni 24 ana fafatawa tsakanin kungiyar jihadi ta Hayat Tahri al-Sham da kungiyar Ahrar al-Sham dake zama  kungiyar 'yan tawaye mai karfin iko a yankin Idlib dake arewa maso yammacin kasar.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama a Siriya sun ce wannan ba shi ne karon farko da 'yan tawayen ke gwabzawa da juna ba, tun bayan da suka karbe iko da Idlib. A yanzu dai yankin na Idlib na cikin yankunan da dakarun gwamnatin Bashar al-Assad ke fatan karbe iko da su daga hannun 'yan tawayen Siriya.