′Yan taliban sun mamaye rabin birnin Kunduz | Labarai | DW | 28.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan taliban sun mamaye rabin birnin Kunduz

'Yan Talibans sun kai hari a gidan yarin birnin Kunduz inda suka sako fursononi da dama. Sannan kuma mayakan sun kafa tutarsu a babban dandanli na wannan birni.

Mayakan kungiyar Taliban sun mamaye fiye da rabin Kunduz sa'o'i kalilan bayan da suka kutsa wannan gari da ke Arewacin kasar Afghanistan. Wannan dai shi ne karon farko da kungiyar da ke da kaifin kishin addini ta samu wannan nasara tun bayan hambarar da gwamnatinta shekaru 14 da suka gabata. Sannan kuma wannan na zama koma baya ga gwamnatin ta Afghanistan da ta dare madafun iko shekara gudana ke nan da ta gabata.

Kakakin rundunar 'yan sanda na Kunduz Sayed Sarwar Hussaini ya bayyana cewar mayakan na Taliban sun kai hari a gidan yarin birnin inda suka sako fursononi da dama ciki har da 'yan Taliban. Sannan kuma wani wanda bai so a bayyan sunansa ba ya ce mayakan sun kafa tutarsu a babban dandanli na Kunduz.

Ita dai gwamnatin ta Afghanistan ta sha alwashin kwato wannan gari daga hannu mayakan na sa kai. Tuni aka bayar da sanarwar cewar mazauna Kunduz suka fara arcewa daga garin inda aka yi karo da kimanin mutune dubu 300 a kan hanyar da ke hade Kabul da Tajikistan.