Yan takife a Afghanistan sun kame jamusawa 2. | Labarai | DW | 19.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan takife a Afghanistan sun kame jamusawa 2.

Wasu jamusawa guda 2, tare da abokan aikin su 5 yan ƙasar Afghanistan, sun yi ƙasa ko bisa a yankin Ghazni, dake tazara kilomita 100 a kudancin Kabul tun jiya laraba.

A wani jawabi da ya gabatar a sahiyar yau, gwamnan jihar ta Ghazni Mirajudeen Pattana, ya ce binciken da su ka gudanar ya hakikance cewar wasu yan takife ne da ba a tantance ba,su ka yi awan gaba da mutanen 7.

Kakakin ministan harakokin wajen Jamus, ya ta tabatar da bacewar jamusawan ,saidai sai bai bayana sunayen su ba.

Kazalika ya ce gwamnati tuni ta shiga aikin ceton su, tare da taimakon hukumomin Afghanistan.

Cemma a watan da ya gabata, yan takifen sun capke wani bajamishi ɗaya, saidai su ka belin sa bayan sati guda na tantanawa.

Kakakin ƙungiyar Taliban Zabiullah Mujaheed,ya nunar da cewa, basu ke da alhakin sace wannan jamusawa ba.