′Yan Somaliya da dama sun halaka a teku | Labarai | DW | 19.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan Somaliya da dama sun halaka a teku

Shugabannin Somaliya sun aike wa al'ummar kasar da sako kan rasuwar 'yan kasar 200 zuwa 300 da suka nitse a teku a kan hanyarsu ta isa Italiya daga kasar Libiya.

Rahotanin suka ce 'yan Somaliyan sun dulmiya ne a tekun Baharrum a yayin da suke kokarin isa kasar ta Italiya ta cikin wani karamin kwale-kwale. Mutuwar ta 'yan Somaliyan ta bayyana ne sakamakon musayar bayanai tsakanin iyalan wadanda suka mutu ta kafar dandalin sada da zumunta.

Sai dai har yanzu babu wasu tabbatattun bayanai daga jami'an tsaron gabar ruwan kasashen Italiya da Girka da Libiya gami da Misira a kan rasuwar matafiyan 'yan Somaliyan.

Da dama daga cikin matafiyan da ke futowa daga nahiyar Afirka da yankin Gabas ta Tsakiya na kauracewa yake-yake gami da 'yunwa domin yin tattaki zuwa kasashen Turai, a yayin da dubun-dubata ke rasa rayukansu sakamakon kifewar jiragen ruwa a teku.