′Yan siyasa na Chadi na tattauna halin da kasar take ciki | Siyasa | DW | 23.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

'Yan siyasa na Chadi na tattauna halin da kasar take ciki

A Geneva wasu 'yan siyasa da wakillan kungiyoyin fararar hula na Chadi sun soma wani taron nazarin yanayin siyasa da matsalolin zamantakewa wadanda kasar ke fama da su a karkashin gwamnatin Idriss Deby.

Taron wakilan 'yan siyasa da na kungiyoyi na Chadi a Geneneva

Taron wakilan 'yan siyasa da na kungiyoyi na Chadi a Geneneva

Tun dai bayan zaben shugaban kasa na 2016 wanda Shugaba Idriss Deby ya lashe a karo na biyar, Chadi ta fada cikin rigingimun siyasa. Ana cikin wannan yanayi ne a shekara ta 2018 gwamnatin kasar ta bi ta hanyar majalisar dokoki ta sabunta kundin tsarin mulkin kasar wanda ya tanadi karin karfin iko ga shugaban Idriss Deby. Lamarin da ya kara zafafa yanayin siyasar kasar da yin illa ga tattalin arzikinta. Kungiyar Utopie Nord-Sud ta Chadi ce dai ta kira wannan taron tattaunawa wanda a tsawon kwanaki biyu zai yi kokarin tantance illahirin matsalolin da Chadi ke fama da su da kuma samar da mafita, da zimmar maido da zamna lafiya da kwanciyar hankali a kasar. Sai dai kuma gwamnatin ta Chadi ba ta halartar taro. 

Sauti da bidiyo akan labarin