Yan Siriya na fatan 2015 za ta zo da canji | Siyasa | DW | 02.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yan Siriya na fatan 2015 za ta zo da canji

'Yan Siriya da suka gujewa rikicin da kasar ke fama da shi sun bayyana fatansu na komawa gida a cikin wannan shekara ta 2015.

'Yan gudun hijira da dama daga kasar Siriya ne dai yanzu haka suka warwatsu a kasashen da ke makotaka da su don tsira da rayukansu sakamakon rikicin da ke wakana tsakanin gwamnatin shugaban Bashar al-Assad da 'yan tawayen da ke fafutuka wajen kawar da gwamnatinsa. Alaa al-Bgaie da ke cikin dubban 'yan gudun hijira a kasar Jordan ya ce duk da rashin tabbas na alkiblar da kasar za ta fuskanta amma shi kam gara masa komawa gida da irin yanayin da suke ciki a sansanin 'yan gudun hijira.

"Ya ce an tarwatsamu an kuma ci mana mutunci na tsawon lokaci. Halin da muke ciki a nan sansanin 'yan gudun hijira bai da dadi. Ba wutar lantarki sannan sauran ababan more rayuwa ba su da kyau, don haka a wannan sabuwar shekarar muna fatan komawa gida, kuma muna fatan ganin zaman lafiya ya tabbata a kasarmu".

Shi kuwa Mohammad Abu Adeeb, da shi ma ke gudun hijira a sansanin 'yan gudun hijira na Deraa, ya ce irin shakulatin bangaro da kasashen duniya suka yi da su ne ya sanya su fatan komawa gida. Abu Adeeb ya ce wani abin takaici shi ne irin yadda ba a ko yin magana kan irin laifukan yakin da ake tafkawa a kasar.

"Duniya ta yi watsi da mu tsawon shekaru hudu. Duniya ta yi shiru kan irin abubuwan da ake yi wa al'ummar Siriya. Muna fatan wannan sabuwar shekarar ta kawo karshen irin zub da jinin da ake yi a kasar Siriya da ma juya mana baya da aka yi na shekaru hudu".

Bashar al-Assad Syrien Präsident 4.12.

Shugaban Siriya Bashar al-Assad

To ba wai Abu Adeeb ne kadai ke nuna takaici dangane da halin da Siriya ke ciki ba, Yahia al-Hraki, da shi ma ya gujewa rikicin kasar na daga jerin mutane da ke kuka da irin halin da kasarsu ta haihuwa ta shiga, inda ya ke cewar fatansu guda dai yanzu bai wuce na ganin bangarorin da ke rikici da juna a kasar sun maida takubbansu cikin kube don ganin an samu zaman lafiya ba.

"Muna fatan shekara ta 2015 za ta kansance shekara ta zaman lafiya a duniya baki daya. Muna fatan bangarori daban-daban na 'yan tawayen kasar za su hade waje guda da sunan juyin juya hali don samun zaman lafiya".

Shi dai rikicin na Siriya da aka shafe shekaru ana yinsa ya yi sanadin rasuwar mutane kimanin dubu 76 a cikin shekarar ta 2014 da ta gabata yayin da mutane sama da dubu 33 ke warwatse a kasashe makota cikin sansanin 'yan gudun hijira bayan da suka fice daga kasar don tsira da rayukansu kamar yadda hukumar kare hakkin bani Adama ta Syrian Observatory for Human Rights ta bayyana.

Sauti da bidiyo akan labarin