′Yan sanda sun tuhumi tsohon Shugaban Faransa | Labarai | DW | 02.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan sanda sun tuhumi tsohon Shugaban Faransa

Sarkozy ya zama tsohon shugaban kasar Faransa na farko da 'yan sanda suka kama domin amsa tambayoyi

Tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya shafe sa'ai 15 yana amsa tambayoyi bisa zargin aikata ba dai dai ba, lokacin da yake rike da madafun ikon kasar. Ana zargin Sarkozy da amfani da mukamunsa ta hanyar da ta saba doka, wajen karbar kudaden yakin neman zaben shekara ta 2007 ta hanyayin da suka sha bambam da dokokin kasar.

Tsohon Shugaba Nicolas Sarkozy ya mulki kasar daga shekara ta 2007 zuwa 2012, kuma wannan ya zama karon farko da 'yan sanda suka tsare tsohon shugaban Faransa, domin ya amsa tambayoyi. Tuni Sarkozy ya musanta duk wani zargin saba ka'ida.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu