´Yan sanda sun awon gaba da jagoran ´yan adawa a Zimbabwe | Labarai | DW | 23.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

´Yan sanda sun awon gaba da jagoran ´yan adawa a Zimbabwe

A ƙasar Zimbabwe an kame shugaban ´yan adawa na ƙasar Morgan Tsivangirai kamar yadda lauyansa ya nunar. A cikin daren jiya ´yan sanda suka yi awon gaba da jagoran na ´yan adawa. A yau laraba jam´iyarsa ta Movement for Democratic Change ta shirya gudanar da zanga-zangar, domin ƙara matsawa shugaba Robert Mugabe lamba da a sake fasalin kundin tsarin mulkin ƙasar wanda zai tabbatar da kamanta adalci a zaɓen shugaban kasa da na ´yan majaliar dokoki da za a yi cikin watan Maris. ´Yan sanda sun haramta zanga-zangar saboda gudun yin artabu.