′Yan sanda na fargabar kai hari a Spain | Labarai | DW | 24.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan sanda na fargabar kai hari a Spain

Rundunar 'yan sandan Spain ta fara bincike bayan da daya daga cikin wadanda ake zargi da tayar da hankali a a shafinsa na Facebook ya yi kira a kaddamar da Jihadi.

'Yan sanda a kasar Spain sun cafke mutanen hudu a arewacin kasar bisa zarginsu da alaka da kungiyoyin da ke da kaifin kishin addinnin Islama kamar yadda ma'aikatar harkokin cikin gida ta bayyana. Fadar mulki ta Madrid ta tsaurara matakan tsaro tun bayan harin da aka kai a birnin Paris da ya yi sanadin kashe mutane 17.

'Yan sanda na zurfafa bincike dan gano ko wadannan mutane da aka kama na da alaka da wani shiri na kaddamar da kai hari kamar yadda ma'aikatar harkokin cikin gidan ta bayyana, Sai dai ba ta bada cikakken bayani kan wannan zargi ba.

Wata majiyar kuma ta fada wa gidan jaridar EI Pais cewa an fara wannan bincike ne makwanni biyu da suka gabata bayan da daya daga cikin wadanda ake zargi ya yi amfani da shafinsa na Facebook wajen bada horo ga wasu tare da neman su kaddamar da Jihadi.