'Yan sanda na ci gaba da yin bincike a Turkiyya
January 2, 2017Talla
Kungiyar IS ta dauki alhakin harin da wani dan bindiga ya kai a wani gidan rawa a birnin Istanbul na Turkiyya a lokacin bukukuwan shiga sabuwar shekara; wanda a ciki mutane 39 suka mutu kana wasu da dama suka rasa rayukansu.A cikin wata sanarwa da kungiyar ta baiyana a shafukanta na sada zumunta ta ce sojinta ne ya kai harin.