1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: An kashe shugaban jam'iyyar APC a Zamfara

Abdourahamane Hassane
February 23, 2019

Dab da lokacin da ake gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu a Najeriyar aka ba da sanarwa cewar 'yan bindiga sun kashe shugaban APC a garin Yondoto na Zamfara.

https://p.dw.com/p/3DyQW
Nigeria Angriff von Nomaden im Bundesstaat Plateau | Sicherheitskräfte
Hoto: Reuters/Reuters TV

A Jihar Zamfara, wasu 'yan bindiga sun hallaka Alh Yusuf Agege, shugaban jam'iyyar APC a gundumar Yandoto, kakakin rundunar 'yan sandan Jihar, SP Shehu Muhd ya tabbatar da afkuwar lamari a wata sanarwa da ya bayyana. Wanda ya ce maharan sun bude ma shugaban jam'iyyar wuta inda nan ta ke ya rasa ransa. Haka kuma maharan sun so su kawo cikas a wasu runfunan zabe a jihar a yayin zaben na wannan Asabar sai dai hakan bai samu nasara ba.