Jami'n tsaro a Iran na ci gaba da dauki ba dadi da masu boren kin jinin gwamnati a sakamakon mutuwar matashiya Mahsa Amini a hannun 'yan sandan da'a a tsakiyar watan Satumba.
Jami'an tsaro sun yi amfani barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu boren kin jinin gwamnati a Jamhuriyar Muslunci ta Iran. Tuni wasu manyan kasashen ciki har da Faransa suka fara nuna adawarsu da matakin amfani da karfin tuwo don murkushe mata masu zanga-zanga.
Bayan Amirka da Kanada, kasashe membobin Kungiyar Tarayyar Turai sun yi na'am da duk wasu matakan ladabtarwa da kungiyar ke shirin dauka a kan hukumomin Iran da ke hankorin murkushe masu boren.
Fiye da mutane 100 ne suka halaka ciki har da kananan yara a cewar kungiyoyin kare hakin bani Adama a kasar ta Iran, tun bayan barkear zanga-zangar kin amincewa da mutuwar matashiya Amini a tsakiyar watan Satumba.