′Yan sanda a Togo sun kashe masu zanga-zanga | Labarai | DW | 20.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan sanda a Togo sun kashe masu zanga-zanga

Jami'an 'yan sanda a Lome babban birnin kasar Togo, sun buda wuta a kan masu zanga-zanga inda suka halaka biyu daga cikinsu, wasu 13 kuwa suka ji rauni, yayin wani boren da suka yi a jiya Asabar.

Jami'an 'yan sanda a Lome babban birnin kasar Togo, sun buda wuta a kan masu zanga-zanga inda suka halaka biyu biyu daga cikinsu, wasu 13 kuwa suka ji rauni, yayin wani boren da suka yi a jiya Asabar. Mutanen dai na zanga-zangar nuna adawa ne da mulkin zuria'ar Gnassimbe na kasar.

Shugaba Faure Gnassimbe da ke kan karaga, na mulki ne tun a shekara ta 2005 bayan mutuwar mahaifinsa Gnassimbe Eyadema da ya mulki kasar tsawon shekaru 38. Dubban jama'a ne dai suka yi zanga-zangar a Lome, suna mai cewa shekaru 50 mutane daya ke mulkin, ya yi yawa, suna mai kiran yin gyara ga tsarin mulki ta yadda zai takaita wa'adin mulki.