Yan sanda a Israila sunce suna da hujjar cajin Shugaban kasar da fyade | Labarai | DW | 16.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan sanda a Israila sunce suna da hujjar cajin Shugaban kasar da fyade

ISRAEL/PRESIDENT

Yan sanda a kasar Israila sunce suna da isassun hujjoji da zasu kama shugaba Moshe Katsav da laifin fyade

Rundunar yan sandan Israila tuni ta bada shawarar cajin shugaban kasar da laifin fyade da almundahana.

Rundunar ta yan sanda ta yanke wannan shawararce bayan ganawa tsakanin masu bincike na yan sanda da antoni janar na kasar Meni Mazuz.

Wata sanarwa da lauyan Katsav Zion Amir ya bayar tayi ikrarin cewa yan sandan basu da ikon mika wannan caji,inda ya ce ada can baya antoni janar din yayi watsi da bukatu da dama da rundunar yan sandan ta bayar na cajin manyan jamian gwamnati da manyan laifuka.

Shugaban na Israila a nashi bangare yayi watsi da wannan batu.