′Yan sanda a Faransa sun kame wasu mutane biyu | Labarai | DW | 14.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan sanda a Faransa sun kame wasu mutane biyu

Mutanen ana zarginsu da alaka da dan bindigar da ya kashe wasu 'yan sanda guda biyu a ranar LItinin.

'Yan sanda a Faransa sun cafke wasu mutane guda biyu na kusa da mutumin da ya bindige wasu 'yan sandar guda biyu a Faransa a garin Magnanville,majiyoyin 'yan sanda sun ce mutumin da ya kai harin wanda dan Faransa ne wanda ke da asilin Maroko mai sunan Larossi Aballa na da shekaru 25.

Kuma daman an taba tsareshi a shekara ta 2011 kana aka yanke masa hukunci a shekara ta 2013 na tsawon shekaru uku na zaman gidan yari da kuma hukuncin watannin shida na jeka ka gyara halinka.Saboda samunshi da laifin hadin kai da wata kungiya da ke sarafa mayaka masu jihadi zuwa Pakistan