′Yan mata 14 sun kuma kubuta a Borno | Labarai | DW | 19.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan mata 14 sun kuma kubuta a Borno

Hukumomi a jihar Borno da ke arewacin Najeriya sun ce ‘yan mata 14 daga cikin daliban nan da aka sace a makarantar sakandare da ke garin Chibok sun kubuto.

Wakilinmu na Gombe Al-Amin Sulaiman Muhammad ya ce kwamishinan ilimi na jihar Borno Musa Inuwa Kubo shi ne ya sanar da hakan, inda yace iyayen ‘yan mata 14 ne suka sanar da gwamnati cewa ‘ya ‘yansu fa sun koma garesu.

Hukumomin jihar ta Bornon sun ce an samu ‘yan matan ne a hanyar Damboa zuwa Biu. Har yanzu dai hankula na tashe a jihar ta Borno kasancewar ba a kai ga iya kubutar da ragowar ‘yan matan ba.

Yanzu haka dai adadin 'yan matan da suka rage a hannun wanda suka sace su sun kai 85, inda jami'an tsaro da 'yan agajin nan na Civilian JTF ke ci gaba da lalubensu.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe