1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan majalisar Jamus da ke da tushe da ketare

October 2, 2013

Kimanin 5% na 'yan majalisa da aka zaba a Bundestag na da tushe da ketare. Sai dai a duk lokacin da aka tabo wannan batu, suna dangantashi da wani nau'i na wariya.

https://p.dw.com/p/19sjg
Hoto: dpa

Ajiyar zuciya Azize Tank ta ke yi a duk lokacin da 'yan jarida suka tambayeta yadda ta ji bayan da aka zabeta 'yar majalisar Tarayyar Jamus a ranar 22 ga watan Satumba. Dalili kuwa shi ne wannan batu na tayar mata da hankali, saboda ta na ganin cewar kamar an mayar da ita 'yan bora daga cikin 'yan majalisu saboda kawai ita 'yar asalin Turkiya ce. Duk da cewa Jamusanci da ta ke ji bai kai na jakin birnin Berlin ba, amma kuma ta na fatan ganin an kai matsayin da babu banbanci tsakanin bajamushen asali da aka zaba da kuma wanda ya ke rike da passport din Jamus.

Ita dai Azize Tank ta daya daga cikin 'yan majalisa 35 da ke da tushe da ketare da aka zaba a Bundestag. Shekaru hudun da suka gabata dai adadinsu bai zarta 11 ba. Yayin da a wannan wa'adin aka samu 'yan majalisa 11 da ke da asali da Turkiya sabanin shekara ta 2009 inda aka samu biyar kadai.Lamarin da ya yi matikar faranta zuciyar Filiz Demirel ta cibiyar da ke bai wa 'yan asalin Turkiya kwarin guywa saboda ta na ganin cewa wani ci-gaba ne mai ma'ana.

Filiz Demirel, Portrait Filiz Demirel, Landtagsabgeordnete der Grünen in Hamburg. Copyright Privat, zugeliefert von Naomi Conrad
Filiz DemirelHoto: Privat

"Daga cikin 'yan majalisa 266, 11 daga cikinsu na da alaka da Turkiya. Ba wani abin da za su canja daga al'amuran da suka samu a can, amma dai za siu rika fada ana ji. kana za su bankado al'amura da suke ci musu tuwo a kwarya."

Su dai 'yan majalisan na Jamus da ke da tushe da ketare, ba wai kan halin da baki ke ciki kama daga yadda za su saje har i zuwa 'yancin kada kuri'a a zaben kananan hukumomin za su mayar da hankali kawai ba, A'a, amma har da batutuwan da suka shafi daukacin Jamus kamar karin haraji ko kuma tallafa wa Girka da kudi domin ta tsaya a kan kafafunta.

Mutlu na da ra'ayin da ya sha banban

Özcan Mutlu ya na daya daga cikin wadanda ke da tushe da ketare da aka zaba karkashin inuwar jam'iyyar The Greens ko kuma les Verts. sabanin Azize Tank, ba ya damuwa idan aka dangantashi da dan majalisa na Jamus da ya ke ta tushe da Turkiya. Maimakaon haka ma dai alfahari ya ke yi da mukamin da ya ke rike da shi a jam'iyyarsu wato kakakin manufofin ilimi na jam'iyyar the greens. Mutlu ya ce gwaggwarmaya ya yi kafin ya kai wannan matsayi

"An daina daukan 'yan takara ko 'yar takara da ke da asali da Turkyia a matsayin dan lele. A gurinmu fito wafafatawa ake yi bil haki da gaskiya. Ba a daga mana kafa, wannan kuwa abu ne mai matikar kyau."

Cemile Giousouf Bundestagskandidatin CDU
Cemile Giousouf ta tsaya karkashin jam'iyyyar CDUHoto: DW/R. Breuer

Shi dai Mutlu ya yi imanin cewar zaben 'yan asalin kasashen waje da aka yi a majalisar dokokin Jamus ta Bundestag zai yi tasiri lokacin da za a kafa gwamnati ta gaba. Ya na mai cewa babu mamaki a samu minista daya da ke da tushe da ketare a gwamntin kawance ta Angela Merkel ko ma dai kananan ministoci guda biyu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal balarabe
Edita: Mohammad Nasiru Awal