1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Libiya na tsere wa rikici

September 4, 2014

Fiye da 'yan Libiya 250,00 suka zama 'yan gudun hijra cikin watanni hudu

https://p.dw.com/p/1D6Rf
Libyen/ Kämpfe /Tripolis
Hoto: Reuters

Wani rahoton MDD ya ce fada tsakanin kungiyoyin tsageru masu dauke da makamai a manyan biranen Libiya biyu na Tripoli da Benghazi, ya tilasta wa mutane 250,000 tserewa daga gidajensu da suka hada da mutane 100,000 da ke zaman gudun hijira a wasu sassan kasar.

Rahoton na wannan Alhamis ya ce cikin mutanen da suka tsere akwai ma'aikata 'yan kasashen ketere. Kasar ta Libiya da ke yankin arewacin Afirka ta fada cikin rudani siyasa da tattalin arziki gami da zamantakewa tun shekara ta 2011 lokacin boren da ya kawo karshen gwamnatin Marigayi Mu'ammar Gaddafi ta fiye da shekaru 40. Tun wannan lokaci kungoyoyin tsageru masu gaba da juna suke cin karensu babu babbaka.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu