′Yan Houthi sun kakkabo jirgin yaki | Labarai | DW | 11.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan Houthi sun kakkabo jirgin yaki

'Yan tawayen Houthi na kasar Yemen sun yi ikirarin kakkabo wani jirgin yaki na rundunar taron dangi da Saudiya ke jagoranta domin kai hare-hare a kasar.

Hare-haren Saudiya da kawayenta a Yemen

Hare-haren Saudiya da kawayenta a Yemen

Ikirarin nasu dai na zuwa ne jim kadan bayan da kasar Maroko da ita ma ta bi sahun masu luguden wutar a kasar ta Yemen, ta sanar da bacewar wani jirgin saman yakinta a Yemen din. Kafar yada labarai ta 'yan tawayen na Houthi Al-Masirah ta ruwaito cewa jami'an tsaron sararin samaniyarta sun kakkabo jirgin yakin ne a Wadi Nushur da ke gundumar Saada, yankin da 'yan Houthi ke da karfin iko. Sun kuma nuna hoton bidiyo na abin da suka bayyana da barakuzan jirgin da suka kakkabo din kewaye da shi kabilun yankin na ta shewa da nuna farin cikin samun nasara.