1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijirar Siriya sun shiga halin ni 'ya su a Masar

November 14, 2012

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya( UNHCR) ta ce za a samu karuwar 'yan gudun hijrar daga Siriya sakamakon kara rincabewar rikicin kasar.

https://p.dw.com/p/16jK5
epa03371287 Syrian children play_s in front of their tent at Zaatari Syrian refugee camp, in Mafraq, Jordan, 27 August 2012. According to the UN refugee agency, the total number of people who have fled Syria to neighboring countries rose to at least 147,000. State Minister for Media Affairs and Communications and Official Government Spokesperson Samih Maayteh said about 2300 people arrived in Jordan the last two days and that growing number of Syrians fleeing the war in their country had stretched the camps that had been recently set up to accommodate them. EPA/JAMAL NASRALLAH +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Kwararrun sun bayyanar da cewa yawansu zai karu zuwa dubu 700 kafin karshen shekarar 2012. A dai halin yanzu 'yan gudun hijrar Siriya kimanin dubu 300 ke zaune a kasashen Turkiya da Jordan da Libanon da kuma Iraki. Kuma ko da yake shugaba Mohammed Mursi ya yi alkawarin ba da taimako ga 'yan gudun hijirar Siriya da ke zaune a kasarsa, to amma 'yan gudun hijrar sun ce sun gaji da gafara sa ba su ga kaho ba.

Matsalar rashin kudin jiyya

Fatima wata 'yar gudun hijira ce daga Siriya da ke kwance kan gadon jiyya inda take shakar iskar Oxygen cikin kowane dakiku shida saboda cewa ita kanta ba ta iya numfashi. Ita dai wannan mata da taimakon mijinta ne ta dan daga rigarta domin gwada wani babban tabo da ke bayanta.Ta ce:

" Wannan tabo na same shi daga wani albarushi da ya taba ni har sai da ya kai ga hantata. Sai da aka rede rabin hantata ta dama kuma ita ta hagun bata aiki sosai sai da naurar shakar Oxygen. Ina fatan samun sauki saboda cewa 'ya'yana ba su girma ba."

Main title: Syrian refugees in Egypt Photo title: Nidal, syrian refugee. Copyright: Ahmed Hamdy, Korrespondent der Arabischen Redaktion in Kairo Schlagworte: Ägypten, Syrien, Syrer, Flüchtlinge, Syrien-Krise
Dan gudun hijrar Siriya a MasarHoto: Ahmed Hamdy

Ita dai wannan mata mai 'ya'ya biyu ta ci karo da harbin bindiga a cikin wata musayar wuta da aka yi tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye a birnin Homs. Jim kadan bayan hakan ne kuma aka yi luguden wuta a unguwar da take- dalilin da ya sa ta arce zuwa birnin Alkahiran Masar tare da iyalinta. Fatima ta ce:

" Mun gudu ne ba tare mun dauki wani abu ba. Ba mu da tufafen da za su ba kariya daga sanyin hunturu. Ba mu da komai."

Shi kuma mijinta cewa yake: "Na zo da kudin da na ajiye amma na kashe su wajen biyan kudin asibiti da sayen magunguna. Wannan maganin na saye shi kan Fan 700 na Masar kwatankwancin Euro 100. Matata na bukatar sabbin kaya.To amma muna rashin kudi. Ko da yake an yi mana karo-karo a masallaci, to amma har yanzu babu wani taimako da muka samu a nan Masar."

Mursi ya saba alkawari

Shi dai shugaban Masar Mohammed Mursi a cikin jawabansa na gidan telebijan ya sha shan alwashin ba da taimakon gaggawa ga 'yan siriya da ya ce suna zaman tamkar 'yanuwa a gareshi.

zu: Bringt Mursi den Ägyptern Gerechtigkeit? Egypt's President Mohamed Mursi attends a meeting at the presidential palace in Cairo October 8, 2012, a day after Mursi's "Al Nhada (Renaissance) project. The project is primarily a economic and social programme comprising of promises the president vowed to fulfil within 100 days of taking office. Mursi has won grudging respect from detractors in his first 100 days by sending the army back to barracks faster than anyone expected and raising Egypt's international profile in several newsmaking visits abroad. Yet his political fortunes and those of the Muslim Brotherhood which propelled him to power may well depend on his delivering on more mundane issues such as easing traffic congestion and bread and fuel shortages by Oct. 7 as promised. REUTERS/Amr Abdallah Dalsh (EGYPT - Tags: POLITICS)
Shugaba Mohammed MursiHoto: Getty Images

"Kullum zancen kenan.To amma wa ya taimka wa 'yan uwa daga Siriya? Babu wani taimako da muka samu ya zuwa yanzu."

Mohammed ya na bayyana fushinsa game da rashin cika wannan alkawari. Wannan mutun haifaffen kasar Siriya tun shekaru 15 da suka gabata ne yake zaune a Jamus. To amma ya je birnin Alkahira ne domin ya taimaka wa danginsa da suka baro birnin Homs. Kimanin 'yan gudun hijrar Siriya guda 250 ne dai yake bai wa taimako a jefe-jefe ta shirya musu wajen barci da abinci da kuma tufafi daga kudin tallafi da yake samu daga cocin Katolila ta Laurentius da ke birnin Berlin. Kuma babu wani abu da gwamnatin Masar da hukumar kula da 'yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya(UNHCR) da ya tuntuba suka yi domin ba 'yan gudun hijrar takardun izinin zama.

Mohammed ya kara da cewa: Ana magana ne game da 'yan kasar Siriya da ke Libanon daTurkiya da Jordan. To amma ba wanda ke ba da kulawa ga 'yan kasar Siriya masu yawan kimanin dubu 150 dake zaune a Masar."

Za a iya sauraron sautin wannan rahoto daga kasa.

Mawallafiya: Cornelia Wegerhoff/ Halima Balaraba Abbas
Edita: MohammadNasiru Awal