′Yan gudun hijirar Siriya sun haure miliyan hudu | Labarai | DW | 09.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan gudun hijirar Siriya sun haure miliyan hudu

Wannan dai shi ne adadin 'yan gudun hijira mafi yawa a wannan zamani a cewar Antonio Guterres na Majalisar Dinkin Duniya.

Flüchtlinge Grenzgebiet Türkei Syrien

'yan gudun hijira daga Siriya

Fiye da al'ummar kasar Siriya miliyan hudu ne ke watse a kasashe makwabta inda suke zama 'yan gudun hijira a yankin, bayan da kasar ta fada yakin basasa. Mutane miliyan daya kuma daga cikin wannan adadi sun fice daga kasar ne watanni goma da suka gabata a cewar Majalisar Dinkin Duniya a ranar Alhamis din nan.

Wannan dai shi ne adadin 'yan gudun hijira mafi yawa a wannan zamani a cewar Antonio Guterres shugaban sashin kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya.

Ya ce wannan adadi na bukatar tallafin al'ummar kasa da kasa a daidai lokacin da rayuwarsu ke kara shiga wani hali na kaka na ka yi.

Cibiyar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniyar ta ce yadda dubban 'yan gudun hijira ke kwarara zuwa Turkiya ya sanya adadinsu ya kai miliyan hudu da dubu goma sha uku watse cikin kasashe makwabtan Siriya.