′Yan gudun hijirar Bangui na cikin wani hali | Labarai | DW | 04.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan gudun hijirar Bangui na cikin wani hali

Hukumomin ba da agaji na Majalisar Dinkin Duniya sun ce mutanen da suka guje wa rikicin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya na kara shiga mawuyacin hali a kasashen da suke tsugune.

Hukumomin suka ce wanda wannan matsala yanzu haka ta fi shafar yara kanana ne wanda ke cigaba da kamuwa da ciwon yunwa domin ko a karshen mako ma yara 15 ne suka rasu bayan da iyayensu suka gujewa halin da ake cikin a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, kuma karancin abinci ne ya yi ajalinsu kamar yadda kakakin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriya ta Afrika ta Tsakiya Melissa Flemin ta shaidawa manema labarai.

Baya ga yunwa da ke barazana ga rayukan yaran, Ms. Flemin ta ce sauran jama'a da ke gujewa rikicin kasar na kamuwa da cutukan da suka hada da zazzabin cizon sauro da gudawa da kuma cutukan da ke da nasaba da nufashi saboda yanayin wuraren da suke zaune.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe