′Yan gudun hijira suna kara tagaiyara | Siyasa | DW | 20.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

'Yan gudun hijira suna kara tagaiyara

Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da rahoto kan halin wahala da 'yan gudun hijira ke kara samu kansu a ciki da karuwar masu gudun hijira da ake samu.

A wannan rana ta 20 ga wtaan Yuni ke zama ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin duba halin da 'yan gudun hijira ke ciki, kuma Filippo Grandi ke zama Kwamishinan kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya ya wanda ya yi bayani kan rahoton shekarar da ta gabata ta 2015 mai rikitarwa.

A lokaci da yake gabatar da rahoton kan 'yan gudun hijira kwamishinan na Majalisar Dinkin Duniya, Filippo Grandi tun farko ya nuna rashin jin dadi da irin labarin da yake tafe da shi, saboda karuwar da aka samu na mutanen da suka rasa matsugunansu.

Grandi ya ce wannan ba abu mai dadin ji ba, musamman idan aka yi la'akari da abubuwan da ake bukata da suka hada da kudade domin taimakon wadanda suke cikin hukuba. Sannan jami'in ya nuna irin girman matsalar, inda ake samu mutane 24 da suke barin matsugunansu cikin kowani minti daya.

Kasar Siriya tana kan gaba wajen samar da 'yan gudun hijira. Rikicin da ake yi zuwa karshen shekarar da ta gabata ta 2015 ya samar da 'yan gudun hijira kimanin milyan 11 da rabi, inda daga ciki milyan 4 da dubu-dari hudu suke cikin kasar, yayin da kimanin milyan shida da dubu-dari shida suka tsallaka wasu kasashe. Kasar Iraki tana da 'yan gudun hijira milyan 4 da dubu-dari-hudu.

Schweiz Filippo Grandi UNHCR

Filippo Grandi kwamishinan kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya

Filippo Grandi kwamishinan kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya ya ce akwai matsalolin kudade na kula da 'yan gudun hijira. Jami'in ya ce bugu da kari shi ne rasa rayuka da ake samu a tekun Bahar Rum na 'yan Afirka masu neman shiga kasashen Turai, abin da ya janyo mutane dubu 10 suka mutu a tekun Bahar Rum kadai, daga shekara ta 2014.A cewarsa jami'in galibin mutane suna tsere wa daga yaki da sauran rikice-rikice.

Sauti da bidiyo akan labarin