Yan gudun hijira sun fara komawa gida a birnin Mogadiscio | Labarai | DW | 11.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan gudun hijira sun fara komawa gida a birnin Mogadiscio

Hukumar Majalisar Ɗinkin Dunia mai kulla da yan gudun hijira ta ce mutanen da su ka tsere daga gidajen su, a sakamakon yaƙin da ya ɓarke a birnin Modasiscio na ƙasar Somalia, sun fara komawa gida.

Saidai wasu da dama kuma sun ce, su da Mogadiscio haihata-haihata, inji ƙungiyar, ta la´akari da tosran da ya kama zukatan su, na sake ɓarkewar wani saban rikici.

A jimilce, mutane dubu 400 su ka ƙauracewa Mogadiscio, domin tsira da rayukan su.

A wani labarin kuma ƙungiyar bada agaji ta Care Intrenational, ta nunar da cewa, ma´aikatan ta 2, da aka yi garkuwa da su a ƙasar ta Somalia,tun ranar laraba da ta wuce, su na cikin ƙoshin lahia.

Ƙungiyar ta shiga tantanwa, domin samun belin wannan ma´aikata.