′Yan gudun hijira na Yarmuk na cikin halin tsaka mai wuya | Labarai | DW | 07.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan gudun hijira na Yarmuk na cikin halin tsaka mai wuya

Kwamitin sulhu na MDD ya bayyana fargabansa dangane da makomar wasu dubban Falasɗinawa a sanssani .

sanssanni na Yarmuk wanda ke kusa da Siriya a 'yan kwanaki baya-baya nan, ƙungiyoyin tsagairu masu yin jihadi suka riƙa kai wa hare-hare, na fuskantar babbar barazana.

A wani taron manema labarai ta bidiyio da Pierre Krahenbuh wani shugaban wata hukumar ta Majalisar Ɗinkin duniya ta 'yan gudun hijira Falasɗinu UNRWA ya yi, ya ce 'yan gudun hijira kusan dubu 18 'yan falasɗinu suka sarƙe a cikin sanssanin waɗanda ke buƙatar samun ɗauki na gaggawa.