'Yan gudun hijira 18 sun halaka a teku
March 6, 2016Talla
akalla mutane 18 sun halaka bayan da jirgin ruwan da ke dauke da su a tuntsire a kusa da gabar ruwan tashar shakatawa ta Didim da ke a Kudu maso Yammacin Turkiyya.
Sai dai Jami'an gabar ruwan Turkiyyar sun ce sun yi nasarar ceto wasu 'yan gudun hijirar 15 da ransu da ke a cikin jirgin wanda ke kan hanyar zuwa kasar Girka.
Kuma sun ce yanzu haka sun aika da jiragen ruwa uku da mai dirar angulu guda su na yawo a yankin domin ceto sauran mutanen da ke da sauran kwana a gaba ko kuma gawarwakin wadanda tekun ta ritsa da su.