1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan fashi sun sace mutane 30 a Kaduna

Mouhamadou Awal Balarabe MNA
June 9, 2018

Wasu 'yan fashi da makami sun sace fiye da mutane 30 tare da kashe mutane biyu a hare-haren da suka kai a kan wata hanyar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna a Arewacin Najeriya.

https://p.dw.com/p/2zCyT
Nigeria

Wasu majiyoyi daban-daban sun nunar da cewar a ranar Jumma'a da magariba 'yan fashi da ke kan babrura suka sace mutane 22 a hanyar Birnin Gwari ciki har da wata mace da jaririnta. Dama kuma sun fara makamancin wannan fashi da safe inda suka sace mutane goma.

Satar mutane domin neman kudin fansa na dada karuwa a Arewacin Najeriya musamman a yankin kan iyakar Kaduna da jihar Zamfara, inda aka nunar da cewar daga nan masu aikata miyagun ayyuka da sace dabbobi ke fitowa. A farkon watan Mayu da ya gabata ma mutane kimanin 100 ne aka sace a cikin kwana biyu a kan wata hanya da ke yankin Birnin Gwari.

Shekaru 10 da suka gabata ne wadannan sace-sacen mutane suka samo tushe a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya mai arzikin man fetu, kafin ya bazu ko'ina a kasar, musamman a jihar Kaduna, inda ake sakosu bayan an biya kudin fansa.