1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun tarwatsa wata cibiyar tsaro a Libiya

Muntaqa AhiwaMarch 16, 2015

'Yan tawayen da ke biyayya ga mayakan IS a Libiya, sun yi ikirarin kai hari kan shelkwatar tsaro da ke kusa da Tripoli babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/1ErJW
Matthew VanDyke Libyien Armee Christen IS
Hoto: Imago/UPI Photo

'Yan tawayen sun ce suka kai hari kan shelkwatar tsaro da ke wani yankin da ke kusa da Tripoli babban birnin kasar, kwanaki kalilan da kai wani harin kan ofishin 'yan sanda.

Wata jakar da ke kunshe da nakiyoyi ce dai ta fashe, inda fashe-fashen suka jikkata jami'an 'yan sanda biyar, daya daga cikinsu ma na cikin mawuyacin hali, kamar yadda wani jami'in tsaron yankin ya shaida wa kamfanin labaran Reuters.

Kungiyoyin masu kaifin kishin addinin da ke rike da wurare da dama a kasashen Siriya da Iraki dai, na amfani da fitintinun da suka kunno kai da suka kai ga kifar da gwamnatin marigayi Shugaba Muammar Ghaddafi na Libiyan, wajen ci gaba da rura wutar tashin hankali a kasar.

'Yan tawayen na Libiya, sun bayyana mubaya'arsu ga kungiyar IS watanni shida da suka gabata.