1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun kashe alkalai a Afganistan

Abdul-raheem Hassan
November 7, 2019

Wasu 'yan bindiga da ake zargin mayakan Taliban ne sun bude wuta kan wata motar alkalai yayin da suke kan hanyar zuwa birnin Kabul daga kudancin kasar.

https://p.dw.com/p/3SeUr
Afghanistan Mindestens zehn Tote bei Bombenanschlag
Hoto: Reuters/Parwiz

Hukumomin kasar sun ce harin ya yi sanadiyar mutuwar alkalai hudu nan take, sai dai babu tabbacin ko harin na da alaka kai tsaye ga alkalan ganin yadda 'yan bindigar suka yi barin wuta lokacin da motar sojoji ke gaban motar alkalan.

Kawo yanzu dai alkalai 66 ne 'yan bindiga suka kashe a kasar Afganistan cikin shekaru biyar kacal.