1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan aware sun tsere daga hannun 'yan sanda

May 4, 2014

Rikicin Ukraine na ɗaukar sabon salo, inda bayan rasuwar mutane sama da 40, yanzu an sako wasu ƙarin magoya bayansu a wani abin da gwamnati ke gani sakaci ne na 'yan sandan ƙasar

https://p.dw.com/p/1BthO
Ukraine prorussische Aktivisten Zusammenstöße in Odessa 4.5.14
Hoto: Reuters

'Yan awaren da ke goyon bayan Rasha a Ukraine, sun kutsa cikin wani ofishin 'yan sanda a Odessa inda suka sako wasu 'yan uwansu su 70, a daidai lokacin da firaministan rikon kwaryar ƙasar Arseniy Yatsenyuk, ke danganta kissan ran Jumma'a kan cin hanci da rashawa da kuma sakaci a ɓangaren 'yan sanda. 'Yan awaren dai sun bai wa wasu 'yan sanda wata 'yar igiya mai ɗauke da launin ruwan goro da baki wanda alama ce ta dakarun sojin Rasha wanda kuma kawo yanzu ita ce alamar nuna waɗanda ke da ra'ayin bijirewa gwamnatin ta Ukraine.

A yanzu haka dai akwai alamar tambaya kan ko dakarun sojin ƙasar da ma 'yan sandan, za su iya shawo kan wannan tarzomar wanda mahukunta Kiev ke zargin cewa akwai hannun Moskow, abin da tuni fadar Kremlin ta ƙaryata.Har yanzu dai al'ummomin da ke kewaye da Ukraine na zama cikin fargaba domin suna hangen cewa ɓarkewar yaƙin basasa a ƙasar zai yi tasiri sosai a nasu ƙasashen.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Abdourahamane Hassane