′Yan aware sun samu nasara a Kataloniya | Labarai | DW | 22.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan aware sun samu nasara a Kataloniya

Gungun jam'iyyun 'yan aware sun samu nasara a zaben yankin Kataloniya na Spain abin da ya sake dawo da yiwuwar samun rikicin siyasa da gwamnatin tsakiya.

Gamayyan jam'iyyun masu goyon bayan yankin Kataloniya ya balle daga kasar Spain sun samu nasara a zaben yankin da aka gudanar a wannan Alhamis da ta gabata. Jam'iyyu uku na 'yan aware sun samu kujerun majala 70, dama kujeru 68 ake bukata domin samun rinayje da ake bukata a wannan majalisa mai kujeru 135.

Tuni tsohon shugaban yankin na Kataloniya Carles Puigdemont wanda yake gudun hijira a Beljiyam ya ce sakamakon zabe ya zama kashedi ga mahukuntan Spain musamman Firaminista Mariano Rajoy, wadanda suka tunbuke shi daga madafun iko kuma suka kira zaben.