1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan aware sun sace sanata a kasar Kamaru

Mouhamadou Awal Balarabe
May 2, 2022

'Yan awaren na yankin Ingilishi na kamaru sun yi garkuwa da wata sanata da aka zaba karkashin tutar jam’iyyar shugaban kasar Paul Biya tare da direbanta a yankin Arewa maso yammacin kasar mai fama da tashin hankali.

https://p.dw.com/p/4Ak0b
Kombibild Kamerun

Wasu majiyoyin soji da na gwamnatin Kamaru sun tabbatar da cewa rassa biyu na 'yan ambazoniya na kungiyar ADF sun sace Sanata Elizabeth Regina Mundi a garin Bamenda tare da yin garkuwa da ita. Sai dai bangaren farko ya bukaci a sako wasu daga cikin 'yan awaren da ake tsare da su, yayin da daya bangaren ke neman kudin fansa. Ita dai Sanatan tana zuwa kauyensu domin halartar jana'iza ne lokacin da 'yan awaren sun yi garkuwa da ita a kan hanya.

Sanata Mundi memba ce na kwamitin koli na jam'iyyar RDPC ko CPDM ta Paul Biya, wanda 'yan aware suke zargi da mayar tsiraru na yankin Arewa maso Yamma da Kudu maso yammacin kamaru saniyar ware. Tun a shekara ta 2017 ne, rikicin ya barke a yankin Ingilishi bayan da gwamnati ta murkushe zanga-zangar neman daidaito tsakanin masu magana da Faransaci da masu maganna da Ingilishi.

Ya zuwa yanzu dai fiye da mutane dubu 6,000 ne suka rasa rayukansu a rikicin yayin da kusan mutane miliyan guda suka yi gudun hijira a cewar kungiyar International Crisis Group (ICG).