′Yan adawar Siriya za su shiga tattaunawa | Labarai | DW | 24.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan adawar Siriya za su shiga tattaunawa

Gamayyar kungiyoyin 'yan adawa a Siriya sun amince da shiga tattaunawar zaman lafiya karkashin jagorancin MDD a Geneva. Tattaunawar da ake fata zai kawo karshen yakin basasa a kasar.

Wata sanarwa da kungiyoyin suka fitar na cewa za su aike da wakilai 50, da za su halarci taron Majalisar Dinkin Duniya kan zaman lafiya da zai gudana a birnin Geneva.

Matakin kungiyoyin ya zo ne yayin da suke ganawa a birnin Riyadh na kasar Saudiyya, da nufin cimma matsaya gabannin ganawa da shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad a ranar 28 ga watan Nuwamba.

Cimma shawo kan kungiyoyin Siriyar ya samu nasara ne a kokarin masu shiga tsakanin na kasa da kasa, da ke kokarin kwantar da wutar rikici tsakanin 'yan adawa da bangaren gwamnati.

A baya dai MDD ta sha shirya tattaunawa da bangarorin biyu amma yana rugujewa. Yakin basasa a Siriya ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula sama da dubu 330,000, tare da tilasawa miliyoyin 'yan kasar tserewa matsugunansu.