′Yan adawan Togo na sake shirin zanga-zanga | Labarai | DW | 12.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan adawan Togo na sake shirin zanga-zanga

Gwammai na jam'iyyun adawa a Togo ne dai suka kira magoya bayansu da a makon gobe su fito ranakun Laraba da Alhamis don gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnatin Faure Gnassingbe.

'Yan adawa a kasar Togo da ke a Yammacin Afirka sun sake jaddada kira na a fita zanga-zanga a mako mai zuwa duk da cewa gwamnatin kasar ta haramta fita gangami na siyasa saboda gudun rikidewarsa zuwa tashin hankali. Gwammai na jam'iyyun adawa ne dai suka kira magoya bayansu da a makon gobe su fito ranakun Laraba da Alhamis don gudanar da zanga-zangar adawa da mulkin mutu ka raba na Faure Gnassingbe da ke kan karagar mulki tun a shekarar 2005.

Shi dai Gnassingbe ya karbi mulki daga mahaifinsa Gnassingbe Eyadema da ya mulki kasar ta Togo tsawon shekaru 38. 'Yan adawa dai na so a takaita wa'adin mulki zuwa shekaru biyar sau biyu ga shugaban kasa, kasancewar sabon tsari da aka fito da shi a kasar ba zai hana Gnassingbe neman mulki ba a shekarar 2020 da 2025.