1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawan Burundi sun bukaci a yi zabe

Ibrahim Ishaq Danuwa Rano/PAWJune 8, 2015

Madugun 'yan adawan Burundi Agathon Rwasa ya yi ikirarin cewa kasarsa za ta yi zabe, babu gudu babu ja-da-baya, kafin 26 ga watan Ogosta.

https://p.dw.com/p/1Fdk7
Burundi Proteste gegen Präsident Nkurunziza Demonstration
Hoto: Getty Images/AFP/J. Huxta

Duk da wannan ikirari dai da yawa sun ce zai yi wahala a yi sahihin zabe idan har babu tabbacin tsaro da 'yancin fadin albarkacin baki ko sakarwa 'yan jarida mara wajen fitar da sahihan labarai.

Bisa dukkan alamu dai, zaben da aka shirya yi ranar 26 ga watan Yuni ba zai yiwu ba bayan da aka shafe watanni ana zanga-zangar nuna adawa da aniyar shuguga Pierre Nkurunziza na tsayawa takara a karo na uku. A yanzu dai an riga an dage zaben 'yan majalisa da na kananan hukumomi, bayan da mutane 30 suka hallaka a wajen boren.

A wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labaran Reuters, Rwasa wanda ke neman kujerar shugabancin kasar, ya ce wajibi ne kasar ta kasance tana da zababben shugaba kafin 26 ga watan Ogosta lokacin da wa'adin shugaba Nkurunziza zai cika.

Sai dai duk da cewa hukumar zaben kasar ta CENI ta ce tana shirin fitar da sabon jaddawali na zaben 'yan majalisa da na kananan hukumomin, amma har yanzu ba ta fara komai dangane da zaben shugaban kasar ba.