′Yan adawa sun ziyarci Hama Amadou | Siyasa | DW | 03.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

'Yan adawa sun ziyarci Hama Amadou

Wasu rahotanni sun tabbatar da shigar da wata sabuwar bukata a gaban kotu ta yi wa Hama sakin talala zancen da kotun ta ce zata yi nazari a kai.

Hama Amadou

Hama Amadou

A Jamhuriyar Nijer kawancen jam'iyyun adawar COPA 2016 ne ya kai wa dan takarar da yake goyon baya na jam'iyyar LUMANA Hama Amadou ziyara a gidan kason da yake tsare na garin Filingue da ke da tazarar kilo mita 180 daga birnin Niamey, Kawancen ya ce ya kai ziyarar ne don kara jaddada goyon bayansa ga dan takarar nasu yana mai cewar da yardar Allah zai iya lashe zaben da ake shirn yi a gaba a ranar 20 ga watan Maris


Ziyarar da kawancen jam'iyyu da ke adawa na COPA2016 suka kaiwa Malam Hama Amadou dan takarar nasu dai na amatsayin irinta ta farko da kawancen ya kaiwa dan takarar har a inda yake tsare don tattaunawa da shi kan shirye-shiryen zabe da ma duba halin da gwanin nasu yake ciki dangance da batutuwan zaben shugaban kasa zagaye na biyu da za'ayi a cikin wannnan watan.


Niger Anschlag auf Hama Amadou Opposition

Tawagar 'yan dawa a Nijer

Kawancen ya ce ya tarar da Malam Hama Amadou a cikin yanayi mai kyau duk ko da yake an kara karfafa jami'an tsaro sannan kuwa hankalin dan takarar nasu na nan daram kamar yadda aka saba Inji Intinikar Allasane Mahamane da ke a kawancen na COPA2016 kuma zasu kai ga nasara duk da tsare musu dan takara.


Sai dai tuni gungun kawancen masu mulki na MRN ke ci gaba da musanta zargin da 'yan adawar keyi na cewar a na ci gaba da tsare Hama Amadoun ne a wani matsayi na siyasa


Niger Sitz der Fraktion der Oppositionspartei Moden Fa Lumana

Ofishin Moden Fa Lumana

Wannan lamarin na zuwa ne a yayin da Hama Amadou inji wasu rahotanni suka tabbatar da shigar da wata sabuwar bukata a gaban kotu ta yi masa sakin talala zancen da kotun ta ce zata yi nazari akai idan Allah ya kai muna rai a ranar 23 ga watan nan da muke ciki, matakin da wasu suke cewar da zai iya kasancewa kurum idan a kayi la'akari da cewar tuni zaben shugaban kasar an kammalashi a wannan lokacin.

Sauti da bidiyo akan labarin