′Yan adawa na kammala tattakin kilomita 400 a Turkiya | Labarai | DW | 09.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan adawa na kammala tattakin kilomita 400 a Turkiya

Jagoran adawa a Turkiya ya shirya kammala tattakin da ya kwaso tsawon kilomita 400 inda za a tsaya a birnin Istanbul, tattaki mai buri na isar da sakon neman gurgunta dimokradiya.

Tattakin mai lakabin "The Justice March" a Turance ya samu goyon baya na dubban al'ummar Turkiya tun bayan da madugun adawar daga jam'iyyar CHP Kemal Kilicdaroglu ya fita a birnin Ankara fadar gwamnatin Turkiya a ranar 15 ga watan Yuni. Wannan tattaki dai na zuwa ne bayan da kotu ta yanke hukuncin shekaru 25 ga wani mamba na jam'iyyar ta CHP saboda ya bada bayanai ga gidan jarida kan labarin fitar da makamai ta jirgin ruwa zuwa Siriya.

Shugaba Erdogan dai da Kilicdaroglu ya kira shi da sunan dan kama karya ya sha bayyana jam'iyyar ta CHP a matsayin masu marawa 'yan ta'adda baya, ya ma so ya hana tattakin da ke zama cikin kwanciyar hankali.

Manyan sakonnnin masu tattakin dai su ne 'yanci da doka da bin shari'a inda suka rika yin tafiya ta kimanin kilomita 20 a kowace rana cikin zafin rana.